Kamata ya yi 'yan Arewa su marawa Shugaba Tinubu baya a zaben 2027 - Shehu Sani
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya magantu kan sake tsayawar takarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Shehu Sani ya bayyana hakanne yayinda yake zantawa da manema labarai a Kaduna,yace a ra’ayin shi, ya kamata arewa su bar wa ‘yan kudu takara a zaben 2027,domin Arewa ta samu shugaban kasa a 2031.
A cewar sa,duk da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa kowane dan kasa damar tsayawa takara amma kamata ya yi 'yan arewa su marawa 'yan kudu baya a zabe mai zuwa.