Ɗaruruwan masu zanga-zanga mabiya addinin kirista da suka saba Ibadar Lahadi a Coci, a wannan karon sun gudanar da wadannan addu'o'in nasu a matattarar zanga-zanga da ake a jihar Plateau.
Wannan ibada ta nuna hadin kai a fili, saboda a lokacin da suke wannan ibada mabiya addinin Musulunci ne ke kewaye da su suna basu kariya.
Ɗaya daga cikin limaman Cocin dake jagorantar majami'ar El-Buba Outreach Ministries da ke Jos, Pastor Isa El-Buba ya jaddada bukatar gwamnatin Najeriya ta kawo ƙarshen yunwa da rashin tsaro da suka addabi 'yan ƙasar.
A ranar Juma'a ma anga yadda mabiya addinin kiristan suka bada tsaro ga Musulumai da ke Sallar Juma'a a lokacin zanga-zanga, wacce aka fara ta ranar Alhamis ɗaya ga watan Agustan nan da muke ciki