Wani gini ya rufta da wata mata, tare da wasu yara Kano

Wani gini ya rufta da wata mata, tare da wasu yara Kano

Rushewar ginin ya faru ne a unguwar Makwarari da ke jihar Kano, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar rugujewar wani gida wanda ya yi sanadin mutuwar wata mata mai suna Balaraba Tijjani mai shekaru 35 da raunata ‘ya’yanta biyu a ranar Juma’a.


SolaceBase ta ruwaito cewa yaran Abdulnasir ne da Abdallah, masu shekaru 11 da 13.


A cewar mijin matar, Tijjani Magaji, ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya fara a daren ranar Alhamis kuma aka ci gaba da yi har safiyar Juma’a ne ya sa ginin ya ruguje.


Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin hukumar kashe Gobara ta Kano,Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa a ranar Juma’a, da misalin karfe 9:30 na safe, daga daga wani ma’aikacin su Ibrahim Isah, cewa wani gini ya ruguje.


Bayan samun labarin, suka aika da 'yan kwana-kwana cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru.


Abdullahi ya bayyana cewa an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a raye kuma an kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin yi musu magani.

Post a Comment

Previous Post Next Post