Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olushegun Obasanjo ya ce rashin samar da aiki yi ga matasan kasar na iya zama wani abin far fargaba

 Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olushegun Obasanjo ya ce rashin samar da aiki yi ga matasan kasar na iya zama wani abin far fargaba


Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda matasa ke tashe-tashen hankula sakamakon rashin aikin yi.


Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.


Yace yana fargabar matasa na cikin tarin matsaloli na rashin ilimi tare da rashin aikin yi,kuma dole sai an tashi tsaye dan gudun kada abin yafi karfin mu indai hakan ta kasance toh addu'a itace kawai magani.


Bayanin nashi ya zo ne biyo bayan zanga-zangar da matasa keyi a fadin kasar kan tsadar rayuwa a fadin kasar.


Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne dai matasa a fadin Nijeriya suka fara zanga-zanga, lamarin da tun a ranar 1 ga watan Agusta ke kara ta'azzara inda aka rika samun rahotanni da tashe-tashen hankula da sace-sace a fadin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post