Ministan yada labarai Mohammed Idris a wata hira da BBC Hausa kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito, ya ce babu jihar da ba ta karbi nata kason ba, ya zuwa yanzu.
Ministan ya ce tun makonni biyu da suka gabata aka kammala rarraba wannan tallafin shinkafa ga jihohin. Inda ya kara da cewa kowane Gwamna a Nijeriya ya tabbatar da amsar wannan tallafi ban da Gwamnan na jihar Gombe.
A Talatar makon jiya, aka jiyo Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya a lokacin da yake ganawa da kungiyoyin fararen hula a jihar na cewa har yanzu wannan sakon tallafin bai zo hannunsu ba daga gwamnatin tarayya.