Tsohon mashawarci na musamman ga marigayi shugaban kasa Shehu Shagari, Tanko Yakasai, ya nesanta kansa daga wani labari da jaridar Punch ta yanar gizo ta wallafa na kafa wata sabuwar kungiyar siyasa mai suna "The League of Northern Democrats."
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 21 ga Agusta, 2024, aka bai wa manema labarai a Kano.
Yakasai ya kara da cewa "Tun da farko ban yi niyyar yin magana game da wannan lamarin ba."
“ina kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton da jaridar Punch Online Media ta bayar, domin ba ni da hannu a cikin masu shirya taron ko kuma kungiyar da ake magana a kai.”