Talauci zai karu idan aka dawo da tallafin mai a Nijeriya - Shugaban NOA

Shugaban Hukumar wayar da kan al’umma ta Nijeriya (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya yi tir da batun dawo da tallafin man fetur, wanda a cewarsa zai kara jefa kasar cikın matsanancin talauci.

Daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar kasa dai a yanzu shi ne dawo da tallafin man fetur. 

Amma a jawabin da ya yi wa kasa baki daya ranar Lahadi, Shugaba Bola Tinubu ya kore dawo da tallafin, inda ya bayyana cire shi matsayin abu mara dadi amma ya zama dole.

Ya kuma kara da cewa tallafin man fetur ya zama kamar wani makamin kashe tattalin arzikin kasar nan kuma abin da ya hana shi cigaba.

Da ya ke magana a wani shirin Gidan Talabijin na Channels Issa-Onilu ya shawarci 'yan Nijeriya kan su tanadi dabarun yadda za su rayu bayan cire tallafin man fetur.

Onilu ya kuma kara da cewa duk wanda ke neman a mayar da tallafin man fetur yana fadin son zuciyarsa ne, ba wani abin da zai taimakawa tattalin arziki ba saboda dole ne a tabbatar da cewa idan an mayar da shi, zai magance matsalar talauci wanda ba zai yi hakan ba sai dai ma ya kara tsananin talauci.

Post a Comment

Previous Post Next Post