Shekaru 15 da Fira-ministar Bangladesh ta kwashe taba mulkin kasar ya zo karshe a Litinin din nan, bayan da zanga-zangar da ke gudana a kasar ta ki ci, ta ki cinyewa.
Sheikh Hasina dai ta tsere ta bar kasar, yayin da sojoji suka bayyana karbe ikon tafiyar da kasar.
Sojojin karkashin jagorancin babban hafsan soji na kasar Waker-Uz-Zaman, sun ce za su kafa gwamnatin rikon kwarya.
Tun a farkon watan Juli dai aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bangladesh da ta yi sanadiyyar mutuwar mutune kusan 100 a ranar Lahadi.
Fira-minista Hasina mai shekaru 76 dai ta fice daga kasar ne a jirgi mai saukar ungulu bayan da masu zanga-zanga suka cika fadarta.