Babbar jami'ar adawa a Najeriya PDP ta ce rashin fitar shugaba Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najeriya ya yi matuƙar baiyanawa cewa gwamnatin jam'iyar APC ba mai tausayin talakawan Najeriya ba ce, duk da yanayi na tausayawa da 'yan ƙasar suka shiga.
A wata sanarwa da mamakin PDP na ƙasa Debo Ologunaba ya fitar jam'iyar ta caccaki shugaba Tinubu tare da nuna buƙatar ya yi jawabi ga 'yan Najeriya yadda za'a fitar da 'yan ƙasa daga ƙangi da suka shiga.
Jam'iyar PDP ta ce saboda yanayi na ƙangi da 'yan ƙasar ke ciki ya sanya suka fara zanga-zanga ranar Alhamis ɗaya ga wannan wata na Augusta amma shugaba Tinubu bai ce uffan ba duk da irin hatsaniya da ake samu a sanadin wannan zanga-zanga.
PDP ta ce Duniya na gani yadda gwamnatin APC ke amfani da jami'an tsaro wurin cin zarafin masu zanga-zanga, tana zargin har ma da kisan wasu daga cikin 'yan zanga-zangar Najeriya.