Shugaba Tinubu zai yi wa kasa jawabi a ranar Lahadi

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya ranar Lahadi 4 ga watan Agustan nan da muke ciki.

A sanarwa da kakakin shugaban kasa Chief Njuri Ngelale ya fitar ta baiyana cewa ana bukatar kafafen yada labarai su jona daga tashar talbijin ta taraiya NTA da gidan radiyon taraiya FRCN domin watsa wannan jawabi na shugaban ƙasa ga 'yan Najeriya.

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu zai fara jawabin ga 'yan ƙasa da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar ta Lahadi sannan za'a maimaita jawabin nasa da misalin ƙarfe 3:00 na yamma da kuma ƙarge bakwai.

Wannan jawabi na shugaban ƙasa dai zai zo ne kwana ɗaya bayan da babbar jam'iyar adawa PDP ta caccaki shugaba Tinubun kan shuru da ya yi, a yayin da aka shiga rana ta uku ana yi wa gwamnatin sa zanga-zangar adawa da tsare-tsaren ta.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp