Shugaba Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin Shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS
Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS).
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al'umma Ajuri Nglele ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Ajayi ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekarar 2018.