Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kudirin dokar karin albashi da alawus-alawus ga manyan ma'aikatan sashen shari'a na kasar.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa Sanata Basheer Lado ya sanar da hakan, inda ya ce wannan ya kara nunawa karara yadda Shugaba Tinubu ya damu da walwala da jin dadin ma'aikatan gwamnatin kasar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa da wannan karin albashi da alawus-alawus, za a rika biyan albashin babban jojin Nijeriya N64m a duk shekara, kenan duk wata zai rika kwasar albashin sama da Naira milyan 5 duk wata.
Shi kuwa alkalin kotun daukaka kara zai rika daukar albashin N62.4m duk shekara, yayin da alkalin kotun koli zai rika daukar albashin N61.4m duk shekara.
Su kuwa alkalan kotunan tarayya da na kotun babbar birnin tarayya da kuma na kotunan kula da ma'aikatan gwamnati, za su rika samun N7.9m a duk shekara.