Ministan Kasafi da kula da lamurran tattalin arzikin Najeriya Atiku Bagudu ya ce shugaba Tinubu na nan yana bibiya tare da nazarin abubuwa da ke faruwa a zanga-zangar da ake yi wa gwamnatin sa.
An samu ƙiraye-kiraye kan shugaba Tinubu ya ce wani game da wannan zanga-zanga a yayin da ta shiga rana ta uku, abinda Bagudu ke cewa ai yana sane sarai da abubuwan da ke wakana.
Ministan ya amince cewa 'yan Najeriya suka cikin mayuyacin hali, amma yana bada tabbacen shugaba Tinubu yana aiki tukuru da zummar ganin an sauƙaƙa wa 'yan Najeriya.