Rundunar 'yan sanda ta sake gayyatar shugaban kungiyoyar kwadago ta kasa (NLC)-Joe Ajaero
Kwanaki biyu bayan ya amsa gayyatar da aka yi masa , rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sake gayyatar shugaban kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma bukaci Emmanuel Ugboaja, babban sakataren kungiyar ta NLC ya bayyana a gabanta tare da Ajaero.
A wata takarda mai kwanan watan Agusta 28, 2024, mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Ibitoye Rufus Alajide, an umurci shugabannin NLC da su gana da mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda a sashin leken asiri na rundunar (FID) da ke Abuja a ranar Alhamis 5 ga Satumba, 2024. .
Wasikar ta bayyana cewa, a ci gaba da gudanar da bincike kan zargin da ake, an bukaci su zo tare da Comrade Emmanuel Ugboaja domin sake samun bayanai.
Benson Upah, jami'in yada labarai na NLC, ya tabbatar da cewa an karbi wasikar ne a ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta.