Rundunar sojin Nijeriya ta girke jami’ai domin kare manoma a wasu jihohin Arewa

Rundunar sojin Nijeriya ta girke jami’ai domin kare manoma a wasu jihohin Arewa




Yayin da aka fara damina, rundunar sojin Najeriya ta ce ta girke sojoji a wasu jihohin arewacin kasar, domin kare manoma daga hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu yayin da suke gudanar da ayyukan su.


A wata sanarwa da daraktan hulda da manema labarai na rundunar Manjo Janar Edward Buba ya fitar ta ce an tura dakarun musamman a jihohin arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.


A cewarsa, matakin ya baiwa manoma da yawa damar samun yin noma don ganin ba a samu matsala ba har zuwa lokacin girbi.


Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da karancin abinci wanda ya kara tabarbare hauhawar farashin kayayyakin abinci da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta bayyana sama da kashi 40 cikin 100.


Post a Comment

Previous Post Next Post