Peter Obi ya musanta jagorantar zanga-zangar Abuja da akace ya yi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben shekarar da ta gabata, Peter Obi, ya musanta cewa ya jagoranci zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa a babban birnin tarayya Abuja ranar 1 ga watan Agusta.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne matasan kasar nan suka gudanar da zanga-zangar kira ga shugaba Bola Tinubu da ya duba halin da suke ciki.
A cewar masu shirya taron, ya kamata a yi zanga-zangar lumana sai dai zanga-zangar ta yi sanadin asarar rayuka da barnata dukiyoyi da kimarsu ta kai na daruruwan miliyoyin naira.
Akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu a manyan biranen wasu jihohin kasar yayin da ake gudanar da zanga-zangar.
Bayan haka, wasu bata gari sun yi amfani da wannan zanga-zangar sun wawure kayayyaki masu mahimmanci na jama'a da sauran mutane.
A cikin sakon da ya fitar ta hanyar X ranar Juma'a, Obi ya ce bidiyon da aka ce an ganshi yana jagorantar zanga-zanga a abuja wani yunkuri ne na bata masa suna.
A cewarsa, an dauki hoton bidiyon ne a ziyarar da ya kai hedikwatar jam’iyyar Labour, inda ya sasanta rikicin da ya barke tsakanin jam’iyyar LP da kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC.
“Wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, wanda ake zaton yana nuna ina jagorantar zanga-zanga a Abuja, shi ma karya ne. A gaskiya an dauki hoton bidiyon ne a ziyarar da na kai Hedikwatar Jam’iyyar Labour, inda na sasanta rikicin da ya barke tsakanin Labour Party da NLC.
Tsohon gwamnan na Anambra ya ce an hada wannan bidiyon ne kawai don bata masa suna,amma bashi da wani sahihancin abin da ake fada akai.