A yayin da al’ummar jihar Kebbi ke shirin tunkarar zaben kananan hukumomi da ke tafe, babbar jam’iyyar adawa a jihar ta PDP ta janye daga shiga zaben.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Bello Suru ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis.
Bello Ya yi zargin cewa shuwagabannin zaben na jiha suna marama jamiyya mai mulki baya, wanda a cewarsa hakan ya bai wa ‘yan takarar APC damar da bai kamata ba.
Ya bayyana cewa PDP ba ta da kwarin gwiwa ga shugabancin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar don gudanar da zaben cikin adalcin.
Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa hukumar zaben ta bukaci yan takara su biya wasu kudade, wanda ta ce ya saba wa ka’idojin shiga zabe a Najeriya.