Nijeriya za ta dauki sabon kocin Super Eagles
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon kocin kasar Sweden Janne Andersson na shirin karbar mukamin sabon kocin Super Eagles.
Andersson mai shekaru 61, wanda ya samu nasarori tare da tawagar kasar Sweden, gami da cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018, an ruwaito cewa NFF ta zabi maye gurbin Finidi George da shi.
Ana saran Andersson ne dai zai jagoranci tawagar 'yan wasan Nijeriya a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2025 mai zuwa.
Har yanzu dai hukumar NFF ba ta tabbatar da nadin a hukumance ba, sai dai majiyoyi na kusa da hukumar na nuni da cewa an kusa fitar da sanarwar.