Nijeriya na daga cikin kasashen da aka fi samun yawan sakin aure - Rahoto


Wani rahoto da shafin yanar gizo na kasar Amurka mai suna Divorce.com  ya lissafa Nijeriya daga cikin jerin kasashen da ke yawan samun mutuwar aure.


Rahotan ya bayyana cewa yawan kisan aure a Nijeriya ya zarta na kasashen Kanada, Indiya, Vietnam, Sri Lanka da kuma kasar Peru.


Alkaluman da aka buga a shafinsu na yanar gizo a watan Yuli, sun nuna cewa Nijeriya ta zo ta goma sha daya cikin kasashe ashirin da shida da aka fi yawan samun matsalar ta mutuwar aure.

Post a Comment

Previous Post Next Post