Nijar ta yi bikin yaye sabbin sojoji hada na kasashen ketare

Nijar ta yi bikin yaye sabbin sojoji hada na kasashen ketare

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar janar Salifou Modi ya jagoranci bikin yaye sabbin kananan sojoji a kwalejin su da ke jihar Agadez a arewacin kasar.


A jimilce dai sabbin dakarun 375 ne da suka hada da na kasar ta Nijar da wasu kasashen Afirka suka kwashe watanni suna samun hora da dubaru na aikin soja.

Daga cikin sojojin kasashen ketaren kuwa da aka yaye a Nijar din akwai biyu na Burkina Faso, biyu na Mali sai na kasashen Sénégal, Cameroun da Guinée.


Wannan yaye sabbin manyan sojoji na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kara fuskantar hare-haren 'yan ta'adda da bullar sabbin kungiyoyin tawaye duk kuwa da ikirarin da hukumomin mulkin sojan na Nijar suke na kawo karshen matsalar tsaro.


To amma wannan na daga cikin matakin da suka sanar na daukan sojoji dubu 10 a ko wace shekara domin tunkarar matsalar.

4 Comments

Previous Post Next Post