Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Taoreed Lagbaja, ya tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa nan ba da dadewa ba sojoji za su shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fama da ita.
Lagbaja ya bayyana hakan ne a Uyo, ranar Alhamis, ya na mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya kudurin su na ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin kasar.