Hukumar tattarawa da rarraba kudaden haraji ta Nijeriya ta ce kowane Sanata cikin sanatocin kasar 109 na karbar albashi da alawus-alawus na ₦1,063,860 a duk wata.
Hukumar ta ba da kididdigar albashi da alawus-alawus din kowane Sanata da cewa tsurar albashin na kamawa ₦168,866:70, sai kudin kula da ababen hawa da zuba musu mai ₦126,650:00, albashin mataimaki na musamman wato P.A ₦42,216:66, albashin ma'aikatan ofis ₦126,650:00.
Sauran su ne kudaden nishadi ₦50,660:00, harkokin yau da kullum ₦50,660:00, kudaden sayo jaridu ₦25,330:00, alawus din suturu ₦42,216,66:00, kudin kula da gida ko masauki ₦8,443.33:00 da alawus-alawus din mazabu ₦422,166:66.
Shugaban hukumar M.B Shehu a cikin wata sanarwa da ya fita, mai kamar martani kan kalaman Sanata Shehu Sani a baya-bayan nan game da batun albashin Sanatoci a Nijeriya da ya yi ikirarin cewa kowane Sanata na karbar N13.5m a matsayin kudaden gudanarwa duk wata.