Muna zargin wasu mutane sun mallaki otal-otal da kudi mallakin jihar Kano a kasashen waje - Barr Muhyi Rimin-Gado



Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta ce ta gano yadda aka sace sama da Naira biliyan 50 daga asusun gwamnatin jihar da na kananan hukumomi  44 na jihar.

Kazalika hukumar ta hannun shugaban ta Barr Muhyi Magaji Rimin Gado, ta ce ta gano yadda aka yi amfani da kudi Naira miliyan 450 domin sayo gidan sauro a magance zazzabin malaria a jihar.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan a wajen taron haras da ma'aikatan gwamnatin jihar, inda ya ce hukumar na kuma bin kadin wasu kadarori da take zargin an yi amfani da kudin sata wajen mallakarsu a Dubai, London da Abuja, ciki kuwa hada otal-otal.

Post a Comment

Previous Post Next Post