Mun toshe jimillar kudaden da suka kai N83bn na wadanda suka dauki nauyin zanga-zanga a Nijeriya - NSA

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya ce ya zuwa yanzu an gano fiye da Naira biliyan 83 na kudin yanar gizo wato cryptocurrency da kuma sauran kudade na zahiri da ake zargin an zuba domin a dauki nauyin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka kammala kwanan nan a fadin Nijeriya.

Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana hakan, yayin gabatar da jawabinsa a taron manyan kasa na Nijeriya da Shugaba Bola Tinubu ya kira a Fadar Aso Rock, Abuja.

Nuhu Ribadu ya shaida cewa kuɗaɗen sun haɗa da dala miliyan $50 na kudin yana gizo (cryptocurrency) daga ciki an toshe dala miliyan $38 a cikin karamin asusun kudi na yanar gizo guda huɗu da kuma Naira biliyan N4 da ake zargin wasu kusoshin 'yan siyasa daban-daban suka bayar a Abuja, Kano, Kaduna, da Katsina.

A cewar wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ɗin ya shaida wa majalisar cewa ana zargin kasashen waje da hannu wajen kitsa daga tutar kasashen waje a yayin zanga-zangar.

Kazalika an gano wani jami'in ƙasashen waje da ke da alaƙa da wannan al'amari, kuma za a ayyana shi a matsayin wanda ake nema nan ba da jimawa ba 'yan sanda za su sanar da hakan a wannan makon.

Post a Comment

Previous Post Next Post