Mun sayo kayayyakin noma na zamani, don kawo ƙarshen yunwa a Nijeriya - Shugaba Tinubu



Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar cewa gwamnati ta sayo kayan noma na biliyoyin Naira dan kawo ƙarshen yunwa a ƙasar.

Tinubu a jawabin da yayi ga 'yan Najeriya Lahadinnan ya ce wannan mataki zai taimaka gãya wurin samar da wadataccen abinci mai rahusa a ƙasar.

Ya kuma ce yana ganawa da gwamnoni da wasu ministoci dan ganin an cimma hakan, sa'annan gwamnati ta raba taki ga manoma inji shugaba Tinubu dan cika wannan buri na gwamnati.

Tinubu ya ce ya fahimci tsanani da ya ingiza jama'a yin zanga-zanga amma duk da haka bai kamata a bari tashin hankali ya daidaita ƙasar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post