Mazauna garin Kano na fuskantar karancin kayan masarufi tun bayan da aka rufe Kasuwanni

Mazauna garin Kano na fuskantar karancin kayan masarufi tun bayan da aka rufe Kasuwanni


Mazauna garin Kano sun ce suna fuskantar karancin kayan masarufi kamar sukari, gari da sauran kayayyaki yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a wasu sassan jihar, wanda hakan yasa kasuwanni da manyan shaguna ke rufe.


Daily Trust ta rawaito cewa bincike ya nuna yadda yawancin shagunan dake unguwanni a Kano kayan su sun kare saboda har yanzu manyan kasuwannin a rufe suke.


Duk da cewa gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita na tsawon sa’o’i shida, amma har yanzu yankuna da dama a cikin babban birnin jihar na fama da karancin kayayyakin masarufi.


Malam Bello Bashir, wani mazaunin Unguwar Sharada da ke karamar hukumar Birni, ya ce a halin yanzu gari da sikari da sauran kayayyaki sun yi karanci a cikin al'umma,kuma hakan yasamo asaline kan rashin bude kasuwanni da ake yi.


Binciken ya kuma nuna cewa farashin kayayyakin da ake da su ya karu sossai domin karancin su da ake samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp