Matsin lamba ne ya sa Shugaba Tinubu ya umurci a kira babbar taron jami'iyyar APC na kasa - Jigon APC


Gamayyar kungiyoyin jami'iyyar APC na shiyyar arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ce umurnin da Shugaba Tinubu ya yi na a kira taron kusoshin jami'iyyar APC na kasa da hakan zai ba da damar a gudanar da babban taron jami'iyyar na kasa, ya biyo bayan matsin lamba da suka yi kan bukatar hakan.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Jos babban birnin jihar Plateau, shugaban gamayyar kungiyoyin Hon Saleh Abdullahi Zazzaga, ya ce sun yi farinciki da shugaban kasa ya aike da wannan wasika ta hannun shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ga shugaban jami'iyyar, Abdullahi Umar Ganduje.

Saleh Abdullahi ya ce a cikin wasikar mai kwanan wata 09/08/2024, ta ba shugaban jami'iyyar zabin kiran taron kusoshin a ko dai 08 ko kuma 19 ga watan Satumba mai kamawa.

Ya ce sun yi murna da jin wannan mataki kasancewar sun jima suna ta kiraye-kirayen da shugaban kasa ya sa baki kan abin da suka kira karfa-karfa da ake shirin yi musu da mukamin shugabancin jami'iyyar da ya subuce musu tun bayan da Abdullahi Adamu ya ajiye.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ya ce idan aka hadu babban taron jami'iyyar na kasa, a nan za su baje hajarsu, su mika kokensu na duk abubuwan da ke damunsu da suke ganin kamar an mayar da su saniyar ware musamman su 'yan arewa ta tsakiyar Nijeriya duk kuwa da abin da ya kira irin wahalar da suka yi wa jami'iyyar APC.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp