Matasa za su ci moriyar gwamnatin Tinubu - Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu na tallafawa da karfafawa matasa ‘yan Najeriya kwarin guiwa wajen yin fice a sana’o’in da suka zaba.
A cewarsa, shugaban kasa yana mutunta matasan Najeriya, kuma jajircewarsa na bayyana a cikin nade-naden mukaman da ya yi da kuma manufofin gwamnati da tsare-tsare irin su asusun zuba jari na matasa, iDICE Programme, da bankin raya matasa na kasa da dai sauransu.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar matasan jam’iyyar APC, karkashin jagorancin shugaban matasan jam’iyyar na kasa Dayo Israel, a ziyarar ban girma da suka kai fadar shugaban kasa.