Masu zanga-zanga zasu sauya akãla zuwa birnin taraiya Abuja daga ranar Litini


Da alama masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu basu gamsu da jawaban da yayi ga 'yan ƙasa ba, a maimakon kawo karshen gangamin, yanzu haka shirin shiga Abuja masu zanga-zangar suke.

Rahotanni sun nuna cewa masu gangamin suna wallafawa a shafin nan mai taken #OccupyAbuja cewa zasu dunguma kuma zuwa birnin taraiyar ƙasar domin cigaba daga inda suka tsaya.

Sauran wallafe-wallafe da aka yi ta yi a shafin na twitter ciki har da na tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam'iyar African Action Congress Omoyele Sowore da sauran su, na nuna alamun zanga zanga zata yi zafi a Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post