Masu zanga-zanga sun sace takardun shari'ar Ganduje a babbar kotun Kano - Gwamnatin jiha

Gwamna Abba kabir Yusuf na jihar Kano ya ce wasu 'yan daba sun yi fashin wasu takardun tuhuma kan zarge-zargen cin hanci da aka shigar da su gaban babbar kotun jihar, waɗanda ke kan tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, iyalansa da wasu na kusa da shi, a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi kwanan nan .

Gwamna Abba ya ce tsohon Gwamnan Ganduje, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, na fuskantar tuhume-tuhume masu yawa a gaban babbar kotun jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yuwan Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara domin duba halin da babbar kotun jihar ta shiga bayan da 'yan daba suka lalata ta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar.

Post a Comment

Previous Post Next Post