Masara ta ƙara kuɗi a wasu kasuwannin sassan Nijeriya


Masara ta sake tashi a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, an sayi buhunta N103,000 a makonnan, bayan da a satin da shuɗe aka saye ta N100,000 daidai a kasuwar.


Sai Mai'adua jihar Katsina ana sayar da ita N90,000 daidai a makon nan, amma a makon daya gabata N88,000 aka sai da buhun.


Ita ma kasuwar Giwa jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya buhun masara ya ƙara N5000, inda aka sai da buhun N88,000 a makon nan, amma a makon jiya N83,000 ne kuɗin buhunta.


Sai kasuwar Dawanau jihar Kano ana sayar da ita N87,000 a wannan satin, yayinda a makon daya gabata aka saya N80-85,000.


A Dandume jihar Katsina N82-85,000 aka sayi buhun a wannan makon, haka nan aka sai da a makon daya gabata.


N85000 aka sai da buhun masara a kasuwannin jihar Adamawa a satin nan,yayin da a satin daya wuce aka saya N80-85000.


Ita kuwa Shinkafar Hausa tafi tsada a wasu daga cikin kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da ke Arewacin Nijeriya,wanda ake saidawa N160,000 cif a makon nan,amma dai farashin ya sha banban a kasuwannin a makon daya gabata,inda a kasuwar Dawanau jihar Kano ka sayar kan kuɗi N157,000,yayin kasuwar Giwa jihar Kaduna aka saya N155,000.


Suma dai kasuwannin jihohin Adamawa da Legas farashin buhun Shinkafa 'yar gida N150,000 ne a wannan mako.bayanda a makon jiya aka saya N148,000 a kasuwannin jihar Adamawa,amma dai a jihar Lagos farashin daya ne dana makon nan.


Haka zalika farashin shinkafa bai sauya tufafi ba a kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya N138-155,000.


N145,000 aka sai da buhun shinkafar Hausa a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan mako da muke shirin fita,amma a makon jiya an sayi buhun N147,000.


To a bangaren Shinkafar waje kuwa tafi tsada a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano da aka saya N98,000 a satin nan,haka kuma aka sai da a makon jiya.


Sai dai,shinkafa 'Yar Gwamnati tafi sauki a kasuwar Dandume jihar Katsina a wannan mako,wanda aka sai da N69,000,bayan da a makon daya wuce aka saya N70,000 daidai.


A Mai'adua jihar Katsinan kuma aka saya N88000-90,000 a wannan satin,amma a satin daya shuɗe N88,000 ne kuɗin buhun.



A kasuwar Giwa jihar Kaduna kuma farashin Shinkafar ta sake tashi a makon nan da aka saya N85,000,bayan da makon daya kare ak sai da N80,000 cif-cif.


To a jihar Adamawa an sai da buhun ta N87000-88000 a makon nan, amma a makon jiya an sayi buhun N75,000,a satin na an samu karin sama N10,000 kenan.


An samu karin N1000 guda kan farashin shinkafar waje a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a satin nan da aka saya N76000 ,yayinda a makon jiya aka sai da N75,000.


Da alamu sai farashin wake ya sake komawa gidansa na jiya, musamman a kasuwar Mile 12 International Market jihar da ke jihar a kudancin Nijeriya,an sayi buhun N220,000 a wannan mako,bayan da a makon jiya aka saya N200,000 daidai,tashin farko an samu karin N20,000.


Sai Adamawa aka saya N176,000-180,000 a satin nan,amma a makon jiya N170-175,000 aka sai da buhunsa.


A kasuwar Giwa jihar Kaduna N170,000 ake sayar da buhun farin wake a satin da ke dab da ƙarewa, bayan da a makon daya shude aka saya N150,000,hakan na nuna cewar farashin waken yayi tashi zabi a kasuwar Giwa jihar Kaduna.


N140,000-160,000 ne aka sai da buhun wake a kasuwar Dandume jihar Katsina a satin nan,amma a makon jiya N140,000-145,000 aka sai da buhunsa.


Sai kasuwar Mai'adua jihar Katsinan aka saya N160,000-170,000 a wannan makon,amma a makon jiya N180,000 cif aka sai da buhunsa.


Farashin waken yayi tashin gwouron zabi a kasuwar Dawanau jihar Kano wanda aka sayar da Buhun N155,000,yayinda a makon jiya aka sai da N135,000


Ga ma'abota cin taliya kuwa, farashin kwalin bai sauya zani dana makon Jiya da aka saya N18,500 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas.


Sai farashin ya ƙara a kasuwar Giwa jihar Kaduna wanda aka sai da kwalinta N19,500 a satin nan, yayinda a makon daya gabata aka saya N17500,an samu karin N2000 kenan a makon nan.


N17700 ake sayar da kwalin taliya a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a mako nan,bayan da a makon daya wuce aka saya N17,500.


An samu sauƙin N500 kan farashin taliya na makon daya gabata a kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya N18,500,amma a makon nan an saya N18,000 cif.


A kasuwar Mai'adua jihar Katsinan N17600 ake sai da kwalin taliya a satin nan,haka batun yake a satin daya gabata.


Ita kuwa kasuwar Dawanau jihar Kano kari aka samu a makon nan da aka saya N18,000, bayan da a makon jiya aka saya N16500.


DCL Hausa A'isha Usman Gebi.

Post a Comment

Previous Post Next Post