Gwamnatin tarayya ta ce manoman citta a Nijeriya sun yi asara da ta kai Naira biliyan 12 sakamakon wata annobar da ta lalata amfanin gonakin su a shekarar 2023.
Karamin ministan noma da samar da abinci, Aliyu Abdullahi ne ya bayyana haka a wajen taron Inshorar aikin gona a Abuja.
Ministan ya ce manoman sun yi asarar sama da kashi 90 cikin 100 na yawan amfanin gonakin da suke noma a kakar bara.