Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Maradi dake janhuriyar Nijar ya yi sanadin rayukan mutane da dama

Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Maradi dake janhuriyar Nijar ya yi sanadin rayukan mutane da dama

Saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a ranar juma'ar nan da ta gabata ya yi sanadin rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu masu yawan gaske.


Rahotanni da wadansu fefen bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani na nuni da yadda ruwan ya yi awan gaba da dukiyoyin al'ummar garin Maradin da kewaye.


Kazalika ambaliyar da mazauna garin ke cewa ba a taba ganin irin ta ba a tarihi ta yi sanadiyyar lalacewar hanyoyi da rubtawar gidaje masu tarin yawa.


Ko da yake a hukumance ba a sanar da adadin asarar da ake fuskanta da rayukan ba amma wasu rahotanni na nuni da cewa mutum 14 ne suka hallaka a cikin wannan ambaliya yayin da kadarori da dukiyoyin al'umma na a kalla bilyoyin Cfa ne suka tafi a cikin ruwan.

Post a Comment

Previous Post Next Post