Majalisar Dattawa na tuhumar wasu hukumomin gwamnati kan batun kudade

Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da kudaden al'umma, ya nuna fushinsa ga shugabannin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da wasu hukumomi a kasar.

Hakan ya biyo bayan kin amsa tambayoyin da aka gabatar musu a rahoton binciken kudin na shekarar 2019.

Shugaban kwamitin, Sanata Ahmed Wadada ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Wadada ya kuma ce halayyar hukumomin da abin ya shafa na kin amsa tambayoyi a cikin rahoton binciken yana janyo cikas tare da yin illa ga burikan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya, Ma’aikatar Tsaro, Kamfanin Sadarwa na Tauraron Dan Adam na Najeriya, da sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post