Ma'aikatan sufurin jiragen sama a fadin Nijeriya na ta shirye-shiryen tsunduma yajin aiki.
Hakan ya biyo bayan nuna adawa da yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da cire kashi 50 cikin 100 daga kudaden shiga na cikin gida na manyan hukumomin sufurin jiragen sama.
Yajin aikin zai fara gudana a ranar 21 ga watan Agusta, 2024, Kamar yadda Daily trust ta rawaito.
Sai dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta yi gargadin cewa shiga yajin aikin zai kawo cikas ga harkokin jirage a fadin kasar.
Kungiyoyin sun bayyana hukuncin nasu ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Agusta 14, 2024, mai taken, “Ceto Jiragen Sama Daga Rushewa”, kuma aka sake su ga manema labarai a ranar Alhamis.
Hukumomin da abin ya shafa a fannin sun hada da NCAA, Hukumar Kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya, Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya, da Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya.