Likitocin sun fara yajin gargadi game da sace abokiyar aikinsu

 Likitocin sun fara yajin gargadi game da sace abokiyar aikinsu



Kungiyar Likitoci ta Nijeriya NARD ta fara yajin aikin gargadi a fadin kasar sakamakon ci gaba da tsare guda daga cikin 'yayan kungiyar da aka sace, Dokta Ganiyat Popoola-Olawale.


A cikin sanarwar da ta fitar a Litinin din nan, kungiyar ta ce ta yanke wannan shawarar ne a yayin wani zaman tattaunawa na musamman da ta gudanar ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, 2024.


Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Dokta Dele Abdullahi Olaitan, Sakatare-Janar, Dokta Anaduaka Christopher Obinna da Sakataren Jama’a da Jama’a, Dokta Egbe John Jonah.


Kungiyar ta ce ta kuduri aniyar shiga yajin aikin gargadi na mako daya a fadin kasar nan daga tsakar dare, karfe 12:00 na safe Litinin 26 ga watan Agusta 2024.


Haka zalika ta nuna rashin jin dadin yadda ake ci gaba da barayi ke cigaba da tsare guda daga cikin su Dakta Ganiyat

Poopola duk da kokarin da hukumomin tsaro da gwamnati suka yi ya zuwa yanzu

akan sakinta.


A baya dai kungiyar ta ba da wa'adin makonni biyu na sakin

Abokiyar aikinsu da aka sace wanda tuni lokacin ya wuce.


An sace Dr Popoola ne a ranar Laraba, 27 ga Disamba, 2023 a cikin National Eye Center Staff Quarters da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.


An dauko ta ne tare da mijinta, Nurudeen Popoola, da kuma dan uwan mijin (Folaranmi), wanda ke zaune tare da su.


Daga baya an saki mijin nata a ranar 7 ga Maris, 2024.



Dr Popoola da Folarin har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.

Post a Comment

Previous Post Next Post