Kwastam sun fitar da ka’idojin shigo da kayan abinci da aka sawwake wa haraji

Hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS), a ranar Laraba, ta sanar da amincewar Shugaba Bola Tinubu don aiwatar da dokar shigo da kayan abinci da suka hadar da shinkafa, masara, gero, alkama, da wake ba tare da haraji ba.

Don morar wannan tsari hukumar kwastam ta ce dole masu shigo da ita suna da kamfani da ya zama an yi rijista da shi a Najeriya.

Kazalika, kamfanin ya kasance kuma yana aiki na tsawon shekaru biyar tare da biyan kudin haraji na tsawon shekarun.

Bugu da kari, kmfanonin da za su shigo da kayan abincin dole ne su mallaki masana'antar surfa shinkafar mai ƙarfin yin ton 100 a kowace rana.

Hukumar ta kuma ce aƙalla kashi 75% na kayan da aka shigo da su dole ne a siyar da su ta kasuwannin kayan masarufi da aka sani.

Daga karshe hukumar ta bayyana cewa idan kamfani ya gaza cika wadannan sharuda to zai biya haraji, haka kuma za a hukunta duk kamfanin da ya fitar da kayan da aka shigo da su wajen Najeriya kafin ko bayan sarrafa su.

Post a Comment

Previous Post Next Post