Kwamitin ya bayyana hakan ne ta wani saƙon murya da shugaban sakatariyar Ambasada Ibrahim Waiya ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bashir A Bashir.
Kwamitin zaman lafiyar ya bayyana takaicin sa da irin yadda matasa ke bada dãma wasu na amfani dasu wajen lalata kadarorin gwamnati da na ƴan kasuwa da sunan siyasa.
Shugaban kamirin Ambasada Waiya ya cigaba da cewa tun farko shugabannin zanga-zangar suna da laifi la'akari da yadda aka bayyana musu Abunda ka iya faruwa idan suka ce sai sun gabatar da wannan zanga-zanga amma sukai burus da kiraye-kiraye suka fita, sai kuma gashi abunda suke hange ya afku.
Ambasada Waiya ya kuma nuna takaicin kwamitin bisa kwashe kayan ofishin hukumar Sadarwa ta ƙasa dake hanyar zuwa gidan gwamnati inda yace ba iya kanawa ne sukai asara ba har da jihohin arewa maso gabas, domin shine guri ɗaya tilo da Najeriya ta samar domin koyar da al'ummar arewa harkokin sadarwa.
A ƙarshe kwamitin na zaman lafiya na jihar Kano yaja hankalin masu tada wannan husuma tare da tunatar dasu gobe ƙiyama domin rai zai girbi duk abinda ya shuka.