Kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta bayyana shirin ta na shiga yajin aiki
Kungiyar malaman jami’o’i ta sanar da gwamnatin tarayya shirin ta na shiga yajin aiki a fadin kasar kamar yadda rahoton jaridar PUNCH ya rawaito.
Wasu majiyoyi daga majalisar zartaswar kungiyar ASUU ta kasa sun tabbatar wa da PUNCH a Abuja hakan a Litinin dinnan.
An fitar da sanarwar ne a karshen taron hukumar da aka gudanar a jami’ar Ibadan, kuma ana sa ran mika kwafin ga ma’aikatun kwadago da ilimi na tarayya.
Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin tarayya.
A ranar 26 ga watan Yuni ne Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya gayyaci kungiyar kwadagon zuwa wani taron tattaunawa kan batutuwan da suka shafi jami’o’i da kuma dakile yajin aikin da suka shirya yi.