Kungiyar ma'aikatan sufurin jigaren ruwa sun amince da 200,000 a matsayin mafi karancin albashi
Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen ruwa, Clearing and Forwarding Employers Association (SACFEA) ta amince da Naira 200,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata a bangaren ruwa.
An cimma yarjejeniyar ce bayan shafe shekaru sama da ashirin ana tattaunawar neman mafi karancin albashin na ma'aikatan.
Adadin ya kai kusan kashi 54 cikin 100 fiye da yadda gwamnatin tarayya ta amince da mafi karancin albashi na N70,000 a baya-bayan nan.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin 2024 ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tayin mafi karancin albashi na ga ma'aikata daga N62,000 zuwa N70,000, tare da tabbatar da cewa za a sake duba shi bayan shekaru uku, maimakon shekaru biyar.
Sai dai a wata gagarumar nasara da aka samu, kungiyar SACFEA da kungiyar ma’aikatan ruwa ta Nijeriya (MWUN) sun sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance a karshen mako a birnin Legas karkashin kulawar ministan harkokin ruwa da tattalin arzikin kasa, Adegboyega Oyetola.
Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaban kungiyar MWUN, Kwamared Adewale Adeyanju, ya ce mafi karancin albashin ma’aikatan ruwa a yanzu ya kai N200,000.
Adeyanju ya ce yarjejeniyar babbar nassarace ga ma'aikatan dake aiki tare da alawus-alawus domin samun walwalar su tare da inganta rayuwar ma'aikatan.