Kungiyar kwadago ta NLC na yin wani taron gaggawa kan wani zargi da ake yi wa shugabanta, Ajaero
Tuni dai wasu shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da suka hada da shugaban ta, Joe Ajaero suka hallara a hedikwatar kungiyar ta NLC domin gudanar da wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa.
Taron dai na zuwa ne biyo bayan kiran da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi wa Ajaero domin gudanar da bincike kan zargin bada kudade wajen aikata ba dai-dai ba da cin amanar kasa da kuma aikata laifuka ta yanar gizo.
Sammacin dai ya umarci shugaban NLC ya gabatar da kansa domin amsa tambayoyi da misalin karfe 10:00 na safiyar yau.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, gidan talabijin na Channels ya ba da rahoton yadda gayyatar NPF ke kunshe a cikin wata wasika mai kwanan wata 19 ga Agusta 2024, kuma mai dauke da sa hannun ACP Adamu Muazu a madadin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma yi gargadin cewa za a bayar da sammacin kama shi idan Ajaero ya ki bin umarnin hukumar.