Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta sauya manufofin da suka sanya 'yan Nijeriya cikin wahalhalu

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta sauya manufofin da suka sanya 'yan Nijeriya cikin wahalhalu

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi kira da a sauya manufofin da suka jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki, lamarin da ya janyo zanga-zanga a fadin kasar.


A cewar wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da babban sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja suka sanyawa hannu a wani taron gaggawa da suka gudanar. 


Sanarwar tace tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2023, Tinubu ya cire tallafin man fetur da kudin wutar lantarki, sakamakon faduwar darajar Naira. Duk da gwamnati ta ce yin gyare-gyaren manufofin ya zama dole domin sake farfado da tattalin arzikin Nijeriya, sai dai da dama daga cikin ‘yan Nijeriya sun fuskanci yunwa da hauhawar farashin kayayyaki saka makon manufofin.


PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa tun bayan zanga-zangar,Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi game da zanga-zangar da aka yi ranar Lahadin da ta gabata amma bai yi wani magana akan abubuwan da mutane sukai zanga-zangar akai ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post