Kotu ta tsare wasu masu zanga-zanga 632 a Kano
Wata kotu a Kano ta bayar da umarnin tsare wasu masu zanga-zanga 632 bisa zargin lalata kadarorin gwamnati da na al'umma a yayin zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.
Ana tuhumar su da laifin hada baki, sata, yin taro ba bisa ka’ida ba,tare da tada tarzoma, da kuma lalata ta abubuwa da dama.
Manyan masu shari’a uku ne suka jagoranci kotun,wadanda suka hada da babban alkali, Ibrahim Mansur-Yola, babbar mai shari’a Hadiza Rabiu-Bello, da alkali, Abba Muttaka-Dandago.
Kotun ta dage zaman har sai ranar 19 ga watan Agusta domin cigaba da sauraran shariar.
Tun da farko, Daraktan shigar da kara na Jiha (DPP), Salisu Tahir, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin da ake tuhumarsu ne a ranar 1 ga watan Agusta.
Ya yi zargin cewa a daidai wannan ranar ne wadanda ake kara a lokacin zanga-zanga, sun barnata dukiyoyin gwamnati da na al'ummar jihar.
"Wadanda ake tuhumar sun shiga cikin shagunan mutane sun yi awon gaba da kayayyakinsu, da dukiyoyi da dama kamar yadda ya shaida
Mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 97, 287, 229, 336, 349 da 247 na kundin laifuffuka.
Yayin da wasu daga cikin wadanda ake tuhumar suka amsa laifinsu, wasu kuma sun musanta aikata laifin.
Da yake zantawa da manema labarai, bayan zaman kotun, babban lauyan gwamnatin jihar, Haruna Isa-Dederi, ya ce gwamnatin jihar ta kafa kotunan tafi da gidanka guda uku domin gurfanar da wadanda ake tuhuma.
Isa-Dederi ya bayyana cewa za a yi nazari kan kundin da ma’aikatar shari’a ta bayar da shawarwarin da suka dace kafin ranar da za a dage cigaba da sauraren karar.