Wata babbar kotu a Abuja ta garƙame wasu asusun bankuna na mutane 32 da wasu kamfanoni da ake zargin sun dauki nauyin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa har zuwa lokacin da za a gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Mohammed ya gabatar, ya umurci bankunan da su kamo masu asusun ajiyar ko duk wani mutum da yake mu'amala da asusun ajiyar.