Kotu ta daure barawon da ya saci allunan sanarwa cikin makabartar a Kano, tare da yi masa bulala 30

Wata kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta umurci da a daure wani matashi mai shekaru 25 Hassan Adamu a gidan yari bayan da ta same shi da laifin satar allunan sanarwa 15 da aka kafe a wata makabarta a jihar.

Kotun dai ta tuhumin matashin da aikata laifuka biyu, na ratse da kuma sata, inda Alkalin kotun Malam Umar Lawal ya yanke hukuncin daurin watanni 6 ga matashin tare da yi masa bulala 30.

Lamarin da ya faru a ranar 21 ga Agustan, 2024, an kai kara wajen ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Gwale a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post