Kashi 25% na ma'aikatan lafiya a Burtaniya 'yan Najeriya ne

 


Ministan lafiya da walwalar jama'a, Muhammad Pate, ya yi ikirarin cewa kashi 25% na ma'aikatan kiwon lafiya a kasar Burtaniya 'yan Najeriya ne.

Da yake bayyana matsalar karancin ma’aikatan kiwon lafiya a Nijeriya, Ministan ya ce kashi 67 na likitocin da Najeriya ta horar duk sun yi hijira zuwa kasar Birtaniya.

Ministan ya kara da cewa duk da babu wata dokar kiwon lafiya da ta hana 'yan kasar yin hijira, amma zama a gida zai fi dacewa.

Post a Comment

Previous Post Next Post