Kamfanin mai na NNPC ya ce kudin da ya biya ba na tallafin man fetur ba ne
Kamfanin mai na Nijeriya (NNPC Ltd.) ya ce bai biya wa kowa tallafin man fetur ba cikin watanni tara da suka gabata.
Babban jami’in kula da harkokin kudi na kamfanin, Alhaji Umar Ajiya ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a Abuja.
Ajiya ya ce kamfanin NNPC yana magance matsalar shigo da motoci na Premium Motor Spirit ne kawai tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya.
Yace a cikin watanni takwas zuwa tara da suka gabata, NNPC bai biya kowa ko kwabo ba a matsayin tallafi,babu wani dan kasuwa da ya karbi kudi daga gare su ta hanyar tallafi.
Yakara da cewa Abin da ya faru shi ne, suna shigo da PMS, wanda aka sauke a kan wani farashi na musamman, kuma gwamnati ta ce su sayar da shi a kan farashi mai sauki.
Ya ce kuma yarjejeniyar tana tsakanin gwamnatin tarayya da Kamfanin NNPC, don haka basu biya wani kudi ba da sunan tallafi.