Kamala Harris ta zabi Tim Walz a matsayin mataimakin ta

Kamala Harris ta zabi Tim Walz a matsayin mataimakin ta

'Yar takarar shugabar kasar Amurka ta jam'iyyar Democrat, Kamala Harris, ta zabi gwamnan jihar Minnesota Tim Walz a matsayin abokin takararta a zaben shugaban kasa 


Harris ta sanar da hakan a ranar Talata, 6 ga Agusta, 2024.


Walz, mai shekaru 60, tsohon sojan Amurka ne kuma tsohon malami, an zabe shi a gunduma mai ra'ayin Republican a majalisar wakilai ta Amurka a 2006 kuma ya yi shekaru 12 kafin a zabe shi gwamnan Minnesota a 2018.

Ana ganin Walz a matsayin gwani wajen iya alaka da fararen fata, masu jefa kuri'a na yankunan karkara wadanda a shekarun baya-bayan nan suka kada kuri'a ga dan takarar Republican Donald Trump, abokin hamayyar Kamala.

Post a Comment

Previous Post Next Post