Kafanin kasar China ya sake kwace jirgin Najeriya a Canada



Kamfanin Zhongshang Fucheng industrial investment Ltd, wani kamfani daga kasar China da ake rikicin kwace jiragen sama uku na shugaban kasa a kasar Faransa da wasu kadarori a wasu kasashen, ya kwace wani jirgin na Najeriya a kasar Canada.

Wannan na zuwa ne bayan kwace jiragen sama uku na shugaban kasa da wata kotu a Faransa ta yi a madadin Zhongshan Fucheng, saboda wata takaddama tsakaninsa da gwamnatin jihar Ogun.

Kamfanin ya bayyana cewa ya yanke shawarar sakin daya daga cikin jiragen ukun domin nuna kyakkyawar niyya, mussamman a wani taro da aka shirya tsakanin shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron.

A ranar Litinin, Tinubu ya tafi Faransa a kan jirgin Airbus A330 da aka saki, duk da takaddamar da ta taso game da sayensa, bayan kamfanin na kasar Sin ya saki jirgin.

Kamfanin na kasar Sin ya samu sauyin mallakar takardun jirgin Bombardier 6000 nau'in BD-700-1A10 daga hukumomin Canada a Montreal, watanni kadan bayan wata kotu a Quebec ta yanke hukuncin da ya ba Zhongshang damar kwace jirgin daga hannun Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post