Kafa hukumar kula da Almajirai zai inganta karatun allo a Nijeriya - Sarkin Musulmi


Mai Alfarma Sarkin Muslimi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba sa zuwa Makaranta,
Dr Muhammad Sani Idris, mutum ne da ke da kwarewa a kan yadda za a magance matsalolin da suka addabi karatun allo da yaran da ba sa zuwa makaranta.

Sarkin Musilmin ya na magana ne yayin da wata tawaga daga hukumar ta ziyarce shi a fadarsa dake Sokoto.

Ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga kudirin hukumar na magance wadannan matsaloli inda ya ce zai tattauna da sarakuna gatgajiya domin samun goyon bayansu. 

Tun da farko,Shugaban Hukumar Almajirai da Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta, Dr Muhammad Sani Idris ya ce twawagar ta sa, ta ziyarci Mai Marataba Sarkin Musulmi ne domin ya sa wa hukumar albarka a wannan aiki na gyara karatun allo, dakuma sa, ko mayar da yara makaranta, tare da koya musu sama’o’i domin dogaro da kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post